Skip to content

Gasar Rubutun Makala

Gasar Rubutun Makala

An kirkiri Gasar Rubutun Makala ta Bakadamiya ne don samar da ingantattun bayanan ilimi a fannoni rayuwa daban-daban cikin harshen Hausa. Gasar na zuwa a kowane 15 ga wata, kuma kowa na iya shiga.

Manufofin gasar

  1. Samar da muhimman bincike da rubutu na kimiyya da tarihi da kuma sauran fannoni cikin harshen Hausa
  2. Inganta tsarin bincike da taskace bayanai da kuma haɓaka ƙwarewar rubutun ilimi cikin harshen Hausa
  3. Haɓaka samuwar muhimman ilimi cikin yarukan Afirka don cigaban nahiyar
  4. Samar da sabon tarin ilimi da bincike na dindindin cikin yarukan Afirka don cigaban duniya

Muhimman bangarorin gasar

Muhimman fannoni da gasar za ta maida hankali akai sun kasance kamar haka:

  • Kimiyya (Physics, Chemistry, Biology, Mathematics)
  • Fasaha (Technology)
  • Lafiya (Health & Medicine)
  • Tarihi (History)
  • Literature (Adabi)
  • Ilimin zamantakewa (Social Science)
  • Sauran fannoni na ilimi

Yadda gasar ke gudana

  1. Kowace ranar 15 ga wata za a zo da muhimmiyar tambaya da ta shafi maudu’an da aka ambata a sama. Kuma tambayar za a dora ta ne a shafin Facebook na Bakandamiya Foundation.
  2. Tambayar za ta buƙaci cikakken bayani irin na rubutun encyclopedia (wato conceptual analysis) da bai yi ƙasa da kalmomi 1500 ba. Ku duba wannan makala a matsayin misalin irin makalar da ake so mutum ya rubuta.
  3. Za a ba wa mahalarta gasar awa 72 (kwanaki 3) daga lokacin da aka dora tambayar don su aiko da amsarsu ko rubutunsu.
  4. Za a aiko da amsar ne ta akwatin sako, wato message inbox, na Facebook page na Bakandamiya Foundation.
  5. Kwamitin alƙalai za su yi nazari bisa ka’idoji su tantance sannan su fitar da rubutu guda ɗaya mafi inganci da ya yi nasara.
  6. Za a sanar da sakamako a ranar 20–25 na kowane wata. Ga jerin wadanda suka yi nasara a gasar a baya.

Abubuwan da kwamitin alkalai za su duba

  1. Gamsassu kuma cikakkun bayanai da misalai – maki 25
  2. Tsarin bayanai da nuna sahihancin bincike – maki 25
  3. Dacewar bayanai, salo da tsari da kuma ka’idojin rubutu – maki 20
  4. Kawo muhimman manazarta (references) da ba su kasa 7 zuwa 10 ko fiye ba – maki 15
  5. Cikan kalmomi 1500 ko fiye da haka – maki 10
  6. Aiko da cikakken amsa a kan lokaci – maki 5

Sauran sharuɗɗa da ƙa’idojin gasar

Ga wasu sauran sharuɗɗa da ka’idoji da za a lura da su don shiga gasar:

  • Mutum biyu ba za su iya shiga gasar a lokaci guda ba.
  • Ba za a karbi amasar da aka yi amfani da rubutun AI ba.
  • Ma’aikatan Bakandamiya Organisation ba za su iya shiga gasar ba.

Kyaututtuka

Akwai awalaja da kyaututtuka ga wanda ya yi nasara kamar haka:

  1. Kautar kuɗi N10,000
  2. Za a ba shi/ta certificate.
  3. Za a buga makalarsa/ta da sunansa/ta a Bakandamiya Encyclopaedia.
  4. Za a lissafo sunnansa/ta a wuri na musamman a website na Bakandamiya Foundation.

Kammalawa

Daga karshe, muna sa ran wannan gasar rubutu ta wata-wata za ta ba da gudummawa wajen cike giɓin ilimi da bincike a harshen Hausa, tare da bunkasa ilimi a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.

Daga karshe, kuna iya following na WhatsApp Channel namu don bibiyan sakonninmu na yau da kullum.

×